Wasanni

'Yan Najeriya sun gaza wajen lashe kyautukan CAF - Amuneke

Tsohon dan wasan Najeriya Emmanuel Amunike.
Tsohon dan wasan Najeriya Emmanuel Amunike. Reuters

Tsohon dan wasan Najeriya na tawagar Super Eagles, kuma mai horar da kasar Tanzania a halin yanzu, Emmanuel Amunike, ya koka bisa gazawar da ‘yan wasan Najeriya ke yi wajen samun kyautukan hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF.

Talla

A cewar Amunike ya kamata ‘yan Najeriya su farga cewa an shafe shekaru masu yawa basa samun kyakkyawan wakilci a duk lokacin da hukumar CAF ke gudanar da bukukuwan karrama ‘yan wasa, kungiyoyin kwallon kafa, da kuma masu horarwa a nahiyar Afrika.

Tsohon dan wasan na Super Eagles ya bayyana haka ne, yayin da yake tsokaci kan bikin bada kyautuka na hukumar ta CAF da ya gudana ranar Talata a birnin Dakar na Senegal, inda Najeriya ta samu kyauta daya kawai, kyautar mafi kwazon tawagar kwallon kafa, tsakanin sauran takwarorinta na kasashen Afrika.

Nwankwo Kanu dai shi ne dan wasan Najeriya na karshe da ya samu nasarar lashe kyautar hukumar CAF ta gwarzon dan wasan kwallon kafar Nahiyar Afrika a shekarar 1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.