Sake fasalta tsarin bayar da kyautar Ballon D'Or daga hukumar CAF

Sauti 10:51
Tambarin hukumar kwallon kafar Afrika -CAF
Tambarin hukumar kwallon kafar Afrika -CAF CAF Online

A makon da ya gabata ne hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta bayar da kyautar ballon d'or na gwarzon dan wasan Afrika a Dakar dake kasar Senegal.Gwarzon dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya sake lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afrika karo na biyu a jere a wani gagarumin biki da ya a Dakar babban birnin Senegal .Salah dan asalin Masar ya yi takarar lashe wannan kuyata ce da abokin taka ledarsa a Liverpool, wato Sadio Mane na Senegal da kuma Pierre-Emerick Aubameyang dan asalin Gabon da ke taka leda a Arsenal.Da dama daga cikin masu lura da lamuran wasanni kwallon kafa ne suka bayyana damuwa kasancewa hukumar Caf ba ta mayar da hankali zuwa yan wasan cikin gida.