Zimbabwe

Zanga-zanga ta barke a Zimbabwe bayan karin farashin man fetur

Bazuwar dubban masu zanga-zangar a manyan titunan kasar na zuwa sa'o'i kalilan bayan matakin gwamnati na kara farashin man fetur a kasar wadda yanzu haka al'umma ke fuskantar matsain rayuwa.
Bazuwar dubban masu zanga-zangar a manyan titunan kasar na zuwa sa'o'i kalilan bayan matakin gwamnati na kara farashin man fetur a kasar wadda yanzu haka al'umma ke fuskantar matsain rayuwa. J Njikizana/A

Daruruwan masu zanga-zanga a Zimbabwe sun datse manyan tituna a babban birnin kasar Harare a wannan Litinin, saboda fusata da matakin shugaba Emmerson Mnangagwa na kara farashin litar man fetur zuwa kusan ninki uku na farashin da suka saba saya.

Talla

Rahotanni na cewa a Bulawayo birni na biyu mafi girma a kasar, sai da ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa, wajen watsa taron wasu gungun matasa da ke zanga-zanga a harabar ofishin babbar kotun kasar ta Zimbabwe.

Zanga-zangar ta barke ne kwanaki biyu, bayan da shugaban na Zimbabwe, ya ce farashin litar mai ya koma dala uku da doriya, kwatankwacin naira dubu 1 da 200 ta Najeriya, daga dala daya, wato dai dai da kusan naira 350.

Matakin kara farashin albarkatun man da gwamnatin Zimbabwe ta dauka, ya zo ne bayan da ta sha alwashin samar da wani sabon kudin kasar cikin shekara daya, domin kawo karshen matsalar tattalin arzikin da ta ke fuskanta, wanda a halin yanzu yawan marasa ayyukan yi a kasar ya kai kashi 80 cikin 100.

Mnangagwa ya ce karin ya zama tilas domin kawo karshen karancin man da kasar ke fuskanta, mafi muni da suka taba fuskanta cikin shekaru 10.

Tuni dai kungiyar kwadagon kasar ta yi kiran soma yajin aikin gargadi na kwanaki uku, a dai dai lokacin da Likitoci da malaman makarantu suka shafe makwanni suna kan na su yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI