Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Alkassoum Abdourahman kan yadda kotun ICC ta wanke Laurent Gbagbo da babban na hannun damansa

Sauti 03:44
Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo.
Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo. Peter Dejong/Pool via REUTERS
Da: Azima Bashir Aminu

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague a yau talata ta sallami tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Bagbo da kuma wani na hannun damansa mai suna Charles Ble Goude, bayan share tsawon shekaru a tsare bisa zargin tayar rikicin da ya biyo bayan zaben kasar daga 2010-2011, inda alkalumma ke cewa an samu asarar rayukan mutane akalla dubu uku.Kotun ta dauki matakin ne saboda a cewarta masu shigar da kara sun gaza gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa mutanen sun aikata laifi. Alkassoum Abdourahman, mai bin diddigin wannan shari’a ce tun daga farko, ga abin da ya ke cewa dangane da wannan hukunci.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.