Bakonmu a Yau

Ahmad Tijjani Lawal kan zanga-zangar kasar Zimbabwe

Sauti 03:36
Wasu da ke zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin Zimbabwe na karin farashin man fetur a birnin Harare. 14/01/2019.
Wasu da ke zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin Zimbabwe na karin farashin man fetur a birnin Harare. 14/01/2019. REUTERS/Philimon Bulawayo TPX IMAGES OF THE DAY

Yau alhamis, Evan Mawarire, shugaban wani cocin kasar Zimbabwe da ke goyon bayan tarzomar da ake yi a kasar ke gurfana a gaban kotu, inda ake zargin sa da tunzura jama’a domin yi wa gwamnatin Emmerson Mnagagwa bore.An dai shafe tsawon kwanaki ana tarzoma a kasar, bayan da gwamnati ta kara farashin man fetur ninkin-ba-ninkin, lamarin da ya yi sanadiyyar cafke mutane da dama a biranen Harare da kuma Bulawayo.Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ahmad Tijjani Lawal dangane da wannan zanga-zanga da ta kazance a Zimbabwe.