Kamaru-Najeriya

Majalisar Duniya ta soki Kamaru kan koro 'Yan gudun hijirar Najeriya

Yanzu haka, Kamaru ta karbi ‘yan gudun hijira sama da dubu 370, cikinsu akwai dubu 100 daga Najeriya.
Yanzu haka, Kamaru ta karbi ‘yan gudun hijira sama da dubu 370, cikinsu akwai dubu 100 daga Najeriya. reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta soki lamirin matakin da Kamaru ta dauka na korar dubban ‘yan gudun hijirar Najeriya da ke neman mafaka a kasar bayan hare-haren kungiyar Boko Haram ya kore su daga muhallansu a jihar Borno ta Arewacin Najeriyar.

Talla

Wata sanarwa daga hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna takaici gami da mamakinta, sakamakon rahotannin da ke nuni da cewa Kamaru ta yi wa duban ‘yan gudun hijira da suka kaura daga jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya korar kare a dai dai lokacin da rikici ke dada kamari a yankunansu.

Hukumar ta nuna matukar damuwarta game da wannan mataki da hukumomi suka dauka a Kamaru, ta na mai cewa halin rashin tabbas da rayuwar ‘yan gudun hijirar da aka maido Najeriya da karfin tuwo zai shiga abin a duba.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma bukaci Kamaru ta dai na kora wadanda rikici ya daidaita zuwa kasarsu Najeriya, inda ta nemi ta ci gaba da manufofinta na karamci da kara.

Yanzu haka, Kamaru ta karbi ‘yan gudun hijira sama da dubu 370, cikinsu akwai dubu 100 daga Najeriya.

A wannan makon ne, dai mutum dubu 9,000 suka tsere daga Najeriyan zuwa Kamaru, bayan harin ranar Litinin da kungiyar Boko Haram ta kai wa garin Rann, mai nisan kilomita 175 daga arewacin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI