Sudan

Masu zanga-zanga sun ci gaba da tattaki a Sudan

Wasu zanga-zanga a Sudan, a kusa da gidan wani dan uwansu da ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga yayin arrangama tsakanin jami'an tsaro da masu bore a Khartoum.
Wasu zanga-zanga a Sudan, a kusa da gidan wani dan uwansu da ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga yayin arrangama tsakanin jami'an tsaro da masu bore a Khartoum. Reuters/M.N. Abdallah

Daruruwan masu zanga zanga ne suka yi jerin gwano bayan halartar jana’izar wani mutum da aka kashe jiya a birnin Khartoum dake Sudan.

Talla

Masu zanga zangar sun kekashe kasa sai shugaba Omar Hassan Al Bashir y asauka daga kujerar sa.

Tarin masu zanga zangar sun ce ba zasu daina ba, kuma basa jin tsoro, yayin da suke tattaki a Yankin Buri da yayi kaurin suna wajen adawa da gwamnatin shugaba Omar Hassan al Bashir.

Faifan bidiyon da ak nada ya nuna maza da mata da suka rufe fuskansu, inda suke sukar gwamnati suka kuma kira ga shugaban kasar ya sauka daga mukamin sa.

Kungiyar kwararru ta mutanen Sudan dake jagorancin zanga zangar a fadin kasar tace mutane 3 aka kashe jiya alhamis sakamakon arangamr da akayi tsakanin su da Yan Sanda, cikin su harda wani yaro da kuma likita.

Mai magana da yawun kungiyar Mohammed al Asbat ya tabbatar da mutuwar mutum na uku.

Hukumomin Sudan basu tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba, sai dai sun bayyana cewar adadin mutanen da suka mutu gaba daya sun kai 24, yayin da kungiyar Amnesty International tace adadin ya zarce 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI