Chadi

Sabuwar dangantaka tsakanin Chadi da Isra'ila

Idriss Déby Shugaban kasar Chadi tareda Firaministan Isra'ila Benjamin Nethanyahu
Idriss Déby Shugaban kasar Chadi tareda Firaministan Isra'ila Benjamin Nethanyahu REUTERS/Ronen Zvulun

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewar kasar sa da Chadi sun sake kulla sabuwar dangantakar diflomasiya bayan katse ta da suka yi a shekarar 1972.

Talla

Netanyahu dake ziyarar Chadi, inda ya gana da shugaba Idris Deby ya bayyana matakin a matsayin mai matukar tasiri.

Shugaba Idris Deby na Chadi ya zama shugaban kasar na farko da ya kai ziyarar aiki Isra'ila inda ya bayyana bude wani sabon babin dangantaka bayan ganawar da ya yi da Firaminista Benjamin Netanyahu.

Shugaban Chadi Idris Deby wanda ziyarar ta shi ke zuwa a bazata zuwa Isra’ila, ita ce karon farko tun bayan dawowar huldar Diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 1972 bayan tun farko sun fuskanci baraka tsakaninsu a shekarun a 1967 sakamakon matsin lambar Isra’ilan ga yankin Falasdinu.

Kasar Chadi mai rinjayen mabiya addinin Islama na daga cikin kasashen yammacin Afrika da yanzu haka ke fuskantar barazanar tsaro, yayin da ko a watan da ya gabata ma sai da ta samu tallafin kayakin yaki dama kudade don fatattakar Boko Haram.

A cewar Netanyahu bayan kammala ganawarsa da Deby a wata tattaunawarsa da manema labarai, lokaci ya yi da za su fadada alaka tsakaninsu da Chadi wadda ke matsayin tsohuwar abokiyar huldarsu.

Ziyarar Netanyahu na zuwa ne bayan irin ta da shugaba Deby ya kai Israila a shekarar da ta gabata.

Majiyar tsaron Chadi sun ce kasar ta sayi makaman zamani daga Israila domin yakar Yan Tawayen da suka addabe ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI