Najeriya-Rahotanni

Ana cike da fargabar amfani da matasa wajen bangar siyasa a Najeriya

Hukumomin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin a tarayyar ta Najeriya sun lashi takobin sanya kafar wando guda da duk wani dan siysa da aka samu na daukar nauyin gusar da hankalin matasan  yayin Zabukan.
Hukumomin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin a tarayyar ta Najeriya sun lashi takobin sanya kafar wando guda da duk wani dan siysa da aka samu na daukar nauyin gusar da hankalin matasan yayin Zabukan. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI

Yayin da zabukan tarayya da na jihohi ke kara karatowa a tarayyar Najeriya, ana ci gaba da nuna fargaba kan yadda ake zargin ‘yan siyasa da bawa matasa miyagun kwayoyi masu gusar da hankali domin amfani da su wajen tashe-tashen hankula.A gefe guda kuma hukumomin yaki da shada fataucin miyagun kwayoyin a tarayyar ta Najeriya sun lashi takobin sanya kafar wando guda da duk wani dan siysa da aka samu na daukar nauyin gusar da hankalin matasan  yayin Zabukan. Wakilinmu na Kano Abubakar Abudlkadir Dangambo ya aiko mana da wannan rahoto game da wannan al’amari.

Talla

Ana cike da fargabar amfani da matasa wajen bangar siyasa a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI