Najeriya-OPEC

Adadin danyen man da Najeriya ke hakowa ya karu - OPEC

Har yanzu dai akwai gibi a adadin man da kasashen kungiyar ta OPEC ke hakowa a baya wanda ya samu sandiyyar raguwar man da kasashen Saudiya da Iran da Libya da kuma hadaddiyar daular larabawa suka yi.
Har yanzu dai akwai gibi a adadin man da kasashen kungiyar ta OPEC ke hakowa a baya wanda ya samu sandiyyar raguwar man da kasashen Saudiya da Iran da Libya da kuma hadaddiyar daular larabawa suka yi. REUTERS/Heinz-Peter Bader

Kungiyar kasashe masu arzikin danyen man fetur OPEC, ta ce Najeriya ta samu ci gaba wajen kara yawan gangar danyen man da ta ke hakowa a kowacce rana, da karin ganga sama da dubu 200,000.

Talla

Rahoton kungiyar ta OPEC ya ce zuwa karshen watan Disamban da ya gabata, yawan gangar danyen man da Najeriya ke hakowa a kowace rana, ya karu daga ganga miliyan 1 da dubu 5 da 79, zuwa ganga miliyan 1 da dubu 7 da 97.

Sauran kasashen da rahoton na OPEC ya bayyana karuwar gangunan man da su ke haka a kowace rana, sun hada da Angola wadda ke biye da na Najeriya wajen yawan danyen man da ta ke fitarwa, wadda rahoton ya ce ta samu hako karin ganga dubu 28, inda a yanzu ta ke fitar da jimillar gangunan man, miliyan 1 da dubu 445 a kowace rana.

Kuwait, wadda ta samu karin ganga dubu 72,000, a yanzu ta na hako jimillar ganga miliyan 2 da dubu 800 da 3 a kowace rana.

Sai kuma kasar Venezuela wadda ta samu ci gaban hako karin gangar danyen man dubu 47, a jimlace kuma a kowace rana ta ke hako miliyan 1 da dubu 511.

Ita kuwa Iraqi, yawan gangar man da ta ke haka ya karu da dubu 10,000, a jimlace kuma kowace rana ta ke hako miliyan 4 da dubu 465.

A karshe, rahoton Kungiyar ta OPEC ya ce a jimlace manbobinta na hako gangar danyen man Fetur miliyan 31 da dubu 58 a kowace rana, wanda kuma an samu raguwar hako ganga dubu 751 da aka saba.

Raguwar da aka samu a cewar rahoton an fuskance shi ne daga kasashen Saudiya, Libya, Iran da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI