Najeriya

Zazzabin cutar Lassa ta sake kuno kai a Najeriya

Hana cin bera ko mu’amala da shi, la'akari da yadda ya ke ci gaba da yada cutar a Najeriya
Hana cin bera ko mu’amala da shi, la'akari da yadda ya ke ci gaba da yada cutar a Najeriya CC0 Public Domain

Ma’aikatar lafiya a Najeriya ta ce an samu asarar rayukan mutane 16 sakamakon sake bullar zazzabin Lassa a wannan wata na Janairu shekarar 2019. A watan Mayu na shekarar 2018 ne hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce anyi nasarar shawo kan Cutar Lassa waddda bera ke yadawa a Najeriya. A cewar WHO a makwanno 6 da suka gabata ana samun raguwar cutar yayinda a yanzu ake da mutane kalilan da ke fama da cutar a kasar wadda ta yi fama da barkewar cutar a baya.

Talla

Sashen yaki da cututuka masu saukin yaduwa na ma’ikatar lafiya a Najeriya, ya ce a jimilce mutane 172 ne aka kebe bisa zaton cewa sun kamu da zazzabin a wannan wata, inda aka tabbatar da cewa 60 daga cikinsu na dauke da cutar ce.

Sashen kiwon lafiya a Najeriya na ci gaba da tanttance hanyoyin shawo kan wannan matsalla tareda  taimakon hukumar lafiya ta Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI