Nijar-Benin

Za a soma aikin shimfida bututun mai daga Nijar zuwa Benin

Za a soma aikin shimfida kataren bututun mai daga Nijar zuwa Jamhuriyar Benin cikin shekarar bana.
Za a soma aikin shimfida kataren bututun mai daga Nijar zuwa Jamhuriyar Benin cikin shekarar bana. La Tribune Afrique

Nijar da Jamhuriyar Benin sun kulla yarjejeniya domin shimfida bututun man fetur da zai tashi daga Nijar zuwa gabar ruwan birnin Cotonou.

Talla

Ministan albarkatun mai na Jamhuriyar Nijar Foumakoye Gado, da takwaransa na ma’adanai daga Jamhuriyar Benin Samou Seidou Adambi ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Yamai.

Minista Foumakoye Gado, ya ce za a fara aikin ne a wannan shekara ta 2019, sai dai gwamnatin Nijar ba ta yi karin bayani a game da makomar shirin shimfida irin wannan bututu da zai tashi daga wani yanki mai suna Agadem zuwa Chadi, kafin ya isa gabar ruwan kasar Kamaru ba, wanda ya kamata a fara tun cikin shekarar da ta gabata.

A shekarar 2013, Nijar ta kulla yarjejeniya da kasashen Chadi da Kamaru kan wannan shiri da aka kiyasta cewa zai lashe kusan dala bilyan 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI