Zimbabwe

Za a binciki yan sandan Zimbabwe kan zargin cin zarafin dan Adam

Zanga-zangar Zimbabwe
Zanga-zangar Zimbabwe REUTERS/Philimon Bulawayo

Gwamnatin Zimbabwe ta sha alwashin gudanar da bincike mai zurfi, kan zarge-zargen da ake yiwa jami’an tsaron kasar na azabtar da jama’a, da kuma yiwa mata fyade, yayin kokarin murkushe boren da ‘yan kasar suka yi kan karin farashin man fetur.

Talla

A farkon makon da ya gabata zanga-zanga ta barke a Zimbabwe ta kuma juye zuwa tarzoma, mako guda, bayan sanarwar shugaba Emmerson Mnangagwa, ta karin farashin man fetur da kashi 150 cikin 100, a dai dai lokacin da kasar ke cikin matsin tattalin arziki.

Boren masu zanga-zangar dai ya gudana a mafi akasarin biranen kasar, kafin daga bisani jami’an tsaro su kawo karshen tashin hankali. Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi jami’an da yin amfani da karfi fiye da kima kan mutane, abinda yayi sanadin rasa rayuka 12, da kuma jikkatar daruruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI