Kamaru-Zabe

Kamaru ta kame jagoran 'yan adawa da ya sha kaye a zaben kasar

Maurice Kamto wanda ke matsayin jagoran adawa bayan shan kaye a zaben kasar ya jagoranci wata zanga-zanga adawa da Paul Biya a karshen makon da ya gabata
Maurice Kamto wanda ke matsayin jagoran adawa bayan shan kaye a zaben kasar ya jagoranci wata zanga-zanga adawa da Paul Biya a karshen makon da ya gabata REUTERS/Zohra Bensemra

Hukumomin kasar Kamaru sun kame shugaban 'yan adawar kasar Maurice Kamto saboda shiga wata zanga zanga da aka yi a karshen mako wadda Yan Sanda suka yi amfani da harsashi wajen tarwatsa ta.

Talla

Rahotanni sun ce Kamto na ci gaba da tinzira jama’a domin adawa da shugaba Paul Biya tun bayan faduwar sa zaben da ya ce an tafka magudi a watan Oktoba, wanda daga bisani ya ce shi ya lashe.

Lauyan Kamto, Agbor Bala ya tabbatar da kama jagoran adawar wanda ya shigar da kara kotun kungiyar kasashen Afirka, ya na kalubalantar sake zaben Biya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.