Afrika

A kan hanyar zuwa Yemen yan Afrika sun mutu a cikin teku

Wasu daga cikin bakin haure da aka ceto
Wasu daga cikin bakin haure da aka ceto REUTERS/Darrin Zammit Lupi

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da baki yan Afirka 130 suka nitse a teku, lokacin da kwale kwalen da suke ciki suka tintsire, sakamakon igiyar ruwa.

Talla

Joel Millman, mai Magana da yawun kungiyar dake kula da kwararar baki ta Majalisar Dinkin Duniya, yace kwale kwalen sun kife ne lokacin da suke kan hanyar zuwa Yemen domin samun aikin yi da kuma inganta rayuwar su.

Jami’an yankin sun yi nasara ceto mutane biyu da rai, tare da tsamo gawawaki 5.

Yemen na daga cikin kasashen da akasarin yan Afrika ke zuwa  cin rani duk da irin  matsallolin da ake fuskanta a cikin kasar dangane da batutuwan da suka shafi kare hakokin bil Adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.