Italiya

Wasu kasashen Turai na shirye don kai dauki ga bakin haure

Wasu daga cikin bakin haure cikin kwale-kwalen roba
Wasu daga cikin bakin haure cikin kwale-kwalen roba STR / AFP

Firaministan Italiya Guiseppe Conte ya ce kasashe 5 sun gabatar da kan su domin kai dauki ga baki 47 da suka makale a gabar ruwan kasar da aka hana su shiga.

Talla

Kungiyar agaji ta Sea-Watch 3 ta ceto bakin da suka isa yankin daga wani kwale kwalen roba sama da mako guda, amma Italyia tace ba zata bari su shiga kasar ta ba.

Conte ya bayyana sunayen kasashen da suka yi tayin karbar bakin da suka hada da Jamus da Faransa da Portugal da Malta da kuma Romania.

Shugaba Emmanuel Macron dake jawabi tare da Firaministan Italiya Guseppe Conte bayan kamala taron kasashen dake kudancin Turai, ya bukaci raba bakin cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI