Nijar-Najeriya

Yan Boko Haram sun kai hari garin Bosso

Garin Bosso na yankin Diffa  a Jamhuriyar Nijar
Garin Bosso na yankin Diffa a Jamhuriyar Nijar ISSOUF SANOGO / AFP

Mayakan Kungiyar boko haram sun harbe mutane 4 har lahira a garin Bosso na jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar.Rahotanni sun ce mayakan sun kai harin ne daren litinin, inda suka cinnawa gidaje da motoci 3 dake dauke da tattasai wuta.

Talla

Yan kungiyar Boko Haram a wannan hari na kokarin kawo cikas zuwa ga manoman tattasai, sashen dake taimakawa wajen shigo da kudi zuwa yankin.

Yankin Bosso ya kasance daya daga cikin yankunan da yan kungiyar Boko Haram suka yawaita kai hare-hare a Jamhuriyar ta Nijar.

Harin na zuwa ne makwanni bayan wani harin sama da kasa da sojoji suka kai wanda ya hallaka mayakan boko haram kusan 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.