Boko Haram-Amnesty

Boko Haram ta kashe mutane 60 a garin Rann na Borno - Amnesty

Tawagar jagoran tsagin kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Tawagar jagoran tsagin kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau © AFP PHOTO / BOKO HARAM

Kungiyar Amnesty International ta ce ta samu gamsassun bayanan da ke tabbatar mata cewar akalla mutane 60 mayakan boko haram suka kashe lokacin da suka kai wani kazamin hari a garin Rann da ke Jihar Barnon Najeriya.

Talla

Kungiyar ta ce na’uarar tauraron dan adam da ta yi amfani da shi ya nuna mata daruruwan gidajen da aka kona, wasu daga cikin su tun lokacin harin shekarar 2017, wadanda mutane ke amfani da su a matsayin mafaka.

Daraktar kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho ta ce sun tabbatar da cewar wannan harin na Rann shi ne mafi muni da kungiyar ta kai na baya bayan nan.

Kungiyar ta bayyana hari kan fararen hular da aka raba da matsugunin su a matsayin laifuffukan yaki, inda ta bukaci hukunta wadanda suka aikata.

Ojigho ta kuma ce bayanan da suka samu daga shaidu lokacin harin, ya ce sojoji sun janye daga garin kwana guda kafin kai harin, matakin da ke nuna gazawar hukuma wajen kare fararen hula.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya ta binciki dalilin janyewar rundunar hadin gwuiwa ta kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Najeriya daga garin wanda ya jefa dubban mutane cikin hadari.

Sai dai tuni kakakin sojin Najeriya Janar Sani Usman Kuka sheka ya musanta batun inda ya ce babu gaskiya a rahoton na Amnesty ya na mai cewa su na nan za su mayar da martini kan batun.

A cewar Kuka sheka, dakarun basu janye daga garin ba, haka zalika babu wasu gidaje da aka kona yayin harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.