Isa ga babban shafi
ICC-Gbagbo

Kotun ICC ta amince da sakin Laurent Gbagbo kan tsauraran sharudda

Masu gabatar da karar na fargabar cewar, idan suka koma gida ba za su je kotun ba lokacin da ake bukatar su, saboda haka suna bukatar zaman su wata kasa da ke makotaka da Netherlands
Masu gabatar da karar na fargabar cewar, idan suka koma gida ba za su je kotun ba lokacin da ake bukatar su, saboda haka suna bukatar zaman su wata kasa da ke makotaka da Netherlands CPI
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Azima Bashir Aminu
1 Minti

Kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ICC ta amince da sakin tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo bisa sharadin cewar ba zai koma kasar sa ba. Hukuncin kotun na zuwa bayan bukatar hakan da gungun masu shigar da kara a kotun suka gabatar.

Talla

Alkalan kotun hukunta manyan laifuffukan da ke birnin Haque sun wanke tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo da shugaban matasan Jam’iyyar sa Charles Ble Goude saboda abinda suka kira rashin kwakkwarar shaidar da za ta sa a daure su.

An dai tuhumi mutanen biyu ne da laifin hannu wajen tashin hankalin da ya yi sanadiyar hallaka mutane akalla 3,000 bayan zaben kasar wanda aka sanar da Alhassan Ouattara a matsayin wanda ya samu nasara, amma Gbagbo ya ce ba zai sauka daga karagar mulki ba.

Kotun na tunanin ci gaba da rike Gbagbo da Ble Goude har sai an kamala sauraron daukaka karar da aka yi kan sakin mutanen biyu, amma masu gabatar da karar sun ce suna goyan bayan sakin su muddin dai Gbagbon ba zai koma gida ba.

Masu gabatar da karar na fargabar cewar, idan suka koma gida ba za su je kotun ba lokacin da ake bukatar su, saboda haka suna bukatar zaman su wata kasa da ke makotaka da Netherlands.

Helen Brady, mai gabatar da kara ya ce ana tunanin kai su Belgium kamar yadda aka yi wa Jean Pierre Bemba na Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo.

Ana saran alkalan su dage yanke hukunci zuwa wani lokaci nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.