Chadi

Dakarun Faransa sun tarwatsa rundunar 'yan tawayen Chadi

Daya daga cikin jiragen yakin Faransa samfurin 'Mirage 2000' da aka yi amfani da su wajen kaiwa mayakan 'yan tawayen Chadi farmaki.
Daya daga cikin jiragen yakin Faransa samfurin 'Mirage 2000' da aka yi amfani da su wajen kaiwa mayakan 'yan tawayen Chadi farmaki. AFP/Ludovic MARIN

Shugaban Chadi Idris Deby ya ce jiragen yakin Faransa sun ragargaza wata katafariyar tawagar mayakan ‘yan tawaye da suka yi yunkuri ketara kan iyakar kasar ta Chadi daga Libya.

Talla

Shugaba Deby ya bayyana haka ne a wannan Alhamis yayin jagorantar taron majalisar zartaswar kasar, inda ya ce ba a samu hasarar ran ko da sojan kasar guda ba, da ke taimakawa dakarun na Faransa.

A cewar Deby, bayan shafe kwanaki uku suna kaiwa ‘yan tawayen farmaki, jiragen yakin Faransa sun yi nasarar tarwatsa motocin yaki 20 daga cikin 50 da mayakan ‘yan tawayen suka yi yunkurin kutsawa cikin kasar ta Chadi da su.

Sai dai kakakin kungiyar mayakan ‘yan tawayen na UFR Yousouff Hamid ya musanta Ikirarin na shugaba Deby, inda ya ce sun yi nasarar kutsawa cikin kasar ta Chadi.

A watan Janairu na shekarar 2009 kungiyoyin ‘yan tawayen takwas na kasar Chadi suka hada gwiwa wajen kafa kungiyar ta UFR da nufin hambarar da gwamnatin shugaba Idris Deby, wanda ya dare shugabancin kasar a 1990 bayan hambarar da tsohon shugaba Hissene Habre.

A shekarar 2008 wasu kungiyoyin ‘yan tawayen Chadi uku da suka taso daga gabashin kasar, sun yi nasarar kutsawa har zuwa gaf da fadar shugaban kasa, kafin daga bisani sojin kasar su yi nasarar watsa su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.