Najeriya-Lassa

Cutar Lassa ta hallaka mutane 57 a sassan Najeriya

Wani mai fama da cutar Lassa a jihar Nasarawan Najeriya
Wani mai fama da cutar Lassa a jihar Nasarawan Najeriya Pulse.ng

Hukumar da ke kula da cutuka masu saurin yaduwa a Najeriya NCDC ta ce daga lokacin da aka samu bullar cutar Lassa da bera ke yadawa a watan jiya kawo yanzu cutar ta hallaka akalla mutane 57 a sassan kasar.

Talla

Hukumar wadda ta ce yanzu haka akwai masu fama da cutar ta Lassa a jihohi 19 na kasar, ta tabbatar gano mutane 275 cikin mutane kusan 800 da ake kyautata zatom suna dauke da cutar, yayinda ta ce ana basu kulawar da ta kamata a cibiyoyin kula da cutar.

A cewar hukumar jihohin Edo da Ondo da ke kudancin Najeriyar su suka fi kamuwa da cutar cikin makwanni biyu da suka gabata, inda aka samu fiye da mutane 40 da suka kamu da zazzabin na Lassa.

Haka zalika a cewar NCDC, akwai kuma jami’an lafiya akalla 9 daga jihohin kasar 4 wadanda suka kamu da Lassa sanadiyyar kula da marasa lafiyan da suka kamu da cutar a asibitoci.

Hukumar ta NCDC wadda ita ke da alhakin kula da cutuka masu saurin yaduwa a Najeriyar tare da wayar da kan jama’a, ta ce har yanzu ta na ci gaba da wayar da kan al’ummar kasar game da alamomin cutar da ma abubuwan da ke haddasa ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.