Tarayyar Afrika

Taron kasashen Afrika zai maida hankali kan 'yan gudun hijira

Sansanin Dadaab mai dauke da 'yan gudun hijirar Somalia da suka tserewa rikicin al Shebaab, a kan iyakar Kenya da Somalia.
Sansanin Dadaab mai dauke da 'yan gudun hijirar Somalia da suka tserewa rikicin al Shebaab, a kan iyakar Kenya da Somalia. REUTERS/Thomas Mukoya

Yau Asabar shugabannin Afrika ke halartar taron kungiyar kasashen nahiyar AU a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Talla

A ranar Alhamis da ta gabata aka soma taron kungiyar ta AU, amma tsakanin ministocin kasashen na Afrika.

Taron a wannan shekara, zai maida hankali ne kan halin da dubban ‘yan gudun hijira ke ciki a kasashen da suka koma, da kuma wadanda rikici ya raba da muhallansu a cikin kasashensu.

Wata kididdigar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta nuna cewa yankin saharar Afrika, na dauke da kashi 26 daga cikin jimillar ‘yan gudun hijira miliyan 25 da dubu 400 dake sassan duniya.

Hukumar ta ce, yawan ‘yan gudun hijira a nahiyar ta Afrika ya karu ne, saboda tashe tashen hankula a kasashen, Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Sudan ta Kudu, Somalia, Jamhuriyar Congo da kuma Burundi.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta kara da cewa, kashi 85 na wadanda rikici ya raba da muhallansu, na zaune ne a kasashe masu tasowa, zalika kasashen Uganda, Sudan da kuma Habasha na cikin kasashen duniya 10 da ke kan gaba wajen baiwa ‘yan gudun hijira masu yawan gaske mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.