Chadi

'Yan tawayen Chadi sun shirya kifar da gwamnatin Déby - Faransa

Ministan harakokin wajen Faransa  Jean-Yves Le Drian.
Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian. REUTERS/Benoit Tessier

Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, ya ce manufar gungun ‘yan tawayen Chadi da jiragen yakin Faransa suka kaiwa hari a farkon watan Fabrairu, ita ce kifar da gwamnatin shugaban kasar Idriss Déby, wanda a cikin gaggawa ya bukaci taimakon Faransa don kaucewa juyin mulkin.

Talla

Le Drian, ya bayyana haka ne lokacin da yake yi wa majalisar dokokin Faransa bayani kan farmakin da dakarun kasar suka kaiwa ‘yan tawayen na Chadi.

Mayakan ‘yan tawayen Kungiyar da ake kira “l'Union des Forces de la Résistance” (UFR) sun shiga kasar ta Chadi ne a cikin watan Janairun da ya gabata daga kasar Libiya inda suke da sansani.

Amma bisa bukatar gwamnatin N'Djamena, Faransa ta yi sawu uku da jiragen yakinta samfarin Mirage 2000 tana luguden wuta kan ayarin ‘yan tawayen da ke cikin motoci kimanin 50.

Ministan harkokin wajen na Faransa ya kara jaddada cewa, shiga tsakanin da Faransar ta yi, bai sabawa dokokin duniya ba, kamar yadda ‘yan adawa a Chadi ke zargi.

A shekarar 2008 wasu kungiyoyin ‘yan tawayen Chadi uku da suka taso daga gabashin kasar, sun yi nasarar kutsawa har zuwa gaf da fadar shugaban kasa, kafin daga bisani sojin kasar su yi nasarar watsa su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI