Nijar-Benin

Hadarin kwale-kwale ya kashe mutane 43 a iyakar Nijar da Benin ta ruwa

Ka zalika bincike ya nuna cewa hadarin ya faru ne sanadiyyar wata kakkarfar Iska da ta taso lokacin da ya ke tsaka da tafiya
Ka zalika bincike ya nuna cewa hadarin ya faru ne sanadiyyar wata kakkarfar Iska da ta taso lokacin da ya ke tsaka da tafiya AFP

Akalla mutane 43 ake kyautata zaton sun mutu yayinda wasu da dama kuma suka bace sanadiyyar nutsewar jirgin kwale-kwalen su da ke makare da jama’a a gabar kogin Neja da ke garin Sambera a yankin kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar gab da kan iyakarta da Jamhuriyar Benin.

Talla

Rahotanni na nuni da cewa hadarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya Laraba, bayan da kwale-kwalen ya yi lodin da ya wuce kima.

Magajin garin Sambera, Oumarou Hassane ya tabbatar da ceto mutane 62 da ransu, sai kuma 43 da suka mutu yayinda ake ci gaba da laluben wasu da suka bace a hadarin.

Oumarou Hassane ya ce jirgin kwale-kwalen ya taso daga garin Gori-Beri na Jamhuriyar Benin ne ya na kuma kan hanyarsa ta zuwa Ouna a Jamhuriyar ta Nijar.

Ka zalika bincike ya nuna cewa hadarin ya faru ne sanadiyyar wata kakkarfar Iska da ta taso lokacin da ya ke tsaka da tafiya.

Jami’an sojin ruwa da na kwana-kwana na ci gaba da aikin ceto baya ga masunta na gargajiya wadanda tun farko, su suka ankarar da jama’a tare da ceto tarin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.