Somalia za ta yi ganawar gaggawa da Burundi kan bukatar janye sojinta

Sojin na Burundi 1000 na daga cikin hadakar sojin da ke yaki da kungiyar al-Shebaab a Somalia
Sojin na Burundi 1000 na daga cikin hadakar sojin da ke yaki da kungiyar al-Shebaab a Somalia REUTERS/Shabelle Media

Shugaban Kasar Burundi da takwaran sa na Somalia sun bukaci gudanar da wani taron gaggawa kan shirin janye dakarun Burundi 1,000 dake aikin samar da zaman lafiiya a Somalia nan da karshen wannan wata.

Talla

Shugaba Pierre Nkurunziza ya ce sun tattauna da shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed kan kiran taron kasashen da suka bada gudumawar sojoji domin nazari kan matakin.

Wata majiya a kungiyar kasashen Afirka ta ce tuni aka rubuta sojojin Burundi da za su fara barin Somalia daga gobe alhamis domin komawa gida.

Rahotanni sun ce ministan harkokin wajen Burundi Ezechiel Nibigira ya ziyarci Masar inda ya gana da shugaban kungiyar kasashen Afirka Abdel Fatah al Sisi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.