Najeriya-Zamfara

Jami'an tsaron Najeriya sun hallaka 'yan bindigar Zamfara 59

Wasu makaman 'yan bindigar kenan da jami'an tsaron Najeriyar suka yi nasarar kwacewa
Wasu makaman 'yan bindigar kenan da jami'an tsaron Najeriyar suka yi nasarar kwacewa Kukasheka

Rahotanni daga jihar Zamfara a Tarayyar Najeriya na cewa jami’an tsaron sa kai na kato da gora sun yi nasarar hallaka ‘yan bindaga 59 a wani gumurzu da suka yi yayin farmakin da ‘yan bindigar suka kai wani yanki na jihar.

Talla

A cewar Bube Shehu, guda cikin jami’an na sa kai sai da suka shafe fiye da sa’o’i 4 suna musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindigar wanda ya kai ga asarar mutanensu guda 7.

Yayin artabun a kauye Danjibga na jihar Zamfara, Bube Shehu ya ce sun samu gagarumin dauki da jami’an sojin Najeriyar wanda ta hakan ne suka yi nasarar kashe ‘yan bindigar 59.

Garin na Danjibga mai nisan kilomita 35 da Gusau babban birnin kasar, ya fuskanci hare-haren ‘yan bindigar a lokuta da dama, ba kuma tare da aike musu jami’an tsaro ba.

Jihar Zamfara dai ta jima ta na fama da rikice-rikicen makiyaya da manoma baya ga garkuwa da mutane da ta yi kamari yayinda a baya-bayan batun ya juye zuwa hare-haren ba gaira babu dalili.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.