Senegal

Macky Sall ya sake lashe zaben shugabancin Senegal

Shugaba Macky Sall na Senegal da ya lashe kujerar shugabancin kasar karo na biyu
Shugaba Macky Sall na Senegal da ya lashe kujerar shugabancin kasar karo na biyu REUTERS/Zohra Bensemra

Shugaban Senegal mai ci Macky Sall ya sake lashe zaben shugabancin kasar da sama da kashi 58% na kuri’un da aka kada a ranar lahadin da ta gabata. Sakamakon wanda shugaban hukumar zabe CNRV Demba Kandji ya sanar a yau, na nuni da cewa Idrissa Seck ne ya zo a matsayin na biyu da sama da kashi 20%.

Talla

A cewar shugaban hukumar zaben na Senegal Demba Kandji duka-duka kashi 66.24 ne yawan masu katunan zabe a kasar suka kada kuri'a, yayinda shugaba mai ci ya samu kashi 68.27.

A bangare guda kuma Idriss Seck wanda wannan ne karo na 3 da ya ke tsayawa takarar shugabancin kasar ya samu kashi 20.50, matakin da ke nuna cewa babu bukatar gudanar da zagaye na biyu na zaben.

Karkashin tanadin dokar zaben Senegal dai dole ne dan takarar da ya yi nasara ya samu akalla kashi 50 na yawan kuri'un da aka kada don kaucewa zuwa zagaye na biyu.

Sai dai tuni bangaren adawa ya kalubalanci sakamakon zaben. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.