Libya

Taron kawo karshen rikicin Libya da kuma shirya zaben kasar

Khalifa Haftar da Fayez Al Sarraj na kasar Libya
Khalifa Haftar da Fayez Al Sarraj na kasar Libya FETHI BELAID, KHALIL MAZRAAWI / AFP

Shugaban gwamnatin Libiya da kasashen Duniya ke goyon baya Fayez al-Sarraj da abokin hamayyarsa da tsagin sojin kasar ke yiwa Biyayya Khalifa Haftar, sun cimma yarjejeniyar shirya zabuka a kasar, da nufin kawo karshen yake-yaken da aka shafe tsawon lokaci ana gwabzawa, bayan hambarar Mu’ammar Ghaddafi.

Talla

Shugabannin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ce a Abu Dhabi, domin dukunle gwamnatoci biyun da suke jagoranta a kasar ta Libya.

Tun a watan Mayu na shekara ta 2018, bangarorin biyu suka cimma yarjejeniyar shirya zabukan na Libya a karshen shekarar, amma sabon fadan da ya barke tsakaninsu ya jinkirta sa hannu da kuma aiwatar da yarjeniniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.