Najeriya-Kamaru

Najeriya ta saba ka'ida wajen mika 'yan awaren Kamaru - Kotu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Kamaru Paul Biya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Kamaru Paul Biya Photo: Stringer/AFP

Kotu a Najeriya ta bayyana mika jagororin ‘yan aware na Kamaru ga hukumomin kasar da Najeriyar ta yi a matsayin abin da ya sabawa shari’a dama kundin tsarin mulkin kasar, la’akari da yadda mutanen suka nemi mafaka kuma aka basu.

Talla

A watan Janairun bara ne Najeriyar ta mika jagororin ‘yan awaren su 47 masu fafutukar ganin yankin mai amfani da turancin Ingilishi ya zama kasa mai cin gashin kanta, wadanda suka gudu daga Kamarun bayan rikicin da ya tsananta.

Hukumar kula da ‘yan gudun hjira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce galibin mutanen 47 sun nemi mafaka kuma an basu a Najeriyar amma kuma lokaci guda aka mika su ga gwamnatin Kamaru don fuskantar hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.