Algeria

Gwamnatin Algeria ta rufe jami'o'in kasar

Wasu daga cikin dubban 'yan Algeria da ke zanga-zangar adawa da tazarcen shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika
Wasu daga cikin dubban 'yan Algeria da ke zanga-zangar adawa da tazarcen shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika AFP/Getty Images

Gwamnatin Algeria ta dauki matakin rufe Ilahirin jami’o’in kasar, makwanni biyu kafin fara hutunsu a hukumance, don dankwafar da aniyar dubban daliban da ke shiga zanga-zangar adawa da tazarcen shugaba AbdelAziz Bouteflika.

Talla

Dubban jama’a dai na ci gaba da yin dandazo a birnin Algiers, tattare da aniyar tilasta kawo karshen shugabancin Bouteflika na tsawon shekaru 20, da a yanzu ke neman wa’adi na biyu.

Rahotanni sun ce jami’an tsaron kasar su kame akalla masu zanga-zanga 195, bisa aikata laifukan fasa shaguna, da kuma tayar da hatsaniya.

A halin da ake ciki, sama da makwani biyu kenan shugaban na Algeria yana kasar Switzerland inda ake duba lafiyarsa.

Tun a shekarar 2013, Bouteflika ya daina fita cikin jama’a bayan kamuwa da ciwon mutuwar barin jiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.