Majalisar Dinkin Duniya-Kenya-Muhalli

Taro kan muhalli ya kankama a Kenya duk da mutuwar mahalartansa a hanya

Wasu Mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya kan yanayi kenan a Kenya
Wasu Mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya kan yanayi kenan a Kenya Reuters/Noor Khamis

Majalisar Dinkin Duniya ta fara taro kan matsalar muhallin da duniya ke fuskanta can a kasar Kenya, sai dai taron na zuwa dai dai lokacin da majalisar ke jimamin tarin jami’anta kusan 22 da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin saman Ethiopian Airlines wanda ke hanyar zuwa Kenya a jiya, galibi kuma jami’an na kan hanyarsu ta zuwa taron na yau ne.

Talla

Taron na kwanaki 5 wanda ya samu halartar wakilan kasashen duniya daban-daban, zai tattauna matsalolin muhallin da ke addabar duniya a yanzu ciki kuwa har da illar ledoji ga muhallin wanda taron zai fi mayar da hankali akai.

Mahalarta taron na birnin Nairobi dai, baya ga wakilan kasashe har da ‘yan kasuwa da wakilan kamfanoni da masana’antu da kuma masu fafutukar kare muhalli dama masu yaki da dumamar yanayi, inda yayin taron Majalisar Dinkin duniya za ta mika bukatar ganin wakilan kasashen da suka hallara sun sanya hannu kan yarjejeniyar rage sarrafa nau’ikan ledar wanda ke illa ga muhallin duniya.

Duk da yadda kasashen duniya ke rage sarrafa nau’in ledar da akalla tan miliyan 300 kowacce shekara amma masu masana sun ce har yanzu akwai tarin leda da robobi marasa amfani akalla tan tiriliyan 5 na yawo a tekunan duniya.

Masana dai na ci gaba da gargadi kan illar da nauikan ledar da kuma dagwalon masana’antu ke haddasawa muhalli.

Siim Kiisler shugaban hukumar kula da muhalli ta Majalisar dinkin duniya, ya ce wannan ne lokacin da ya dace duniya ta hada hannu don yakar illar da ledar ke haifarwa muhalli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.