Najeriya-Zamfara

Sojin Najeriya sun hallaka 'yan bindiga 55 a Zamfara

Wasu sojin Najeriya da ke cikin rundunar ta Sharan daji
Wasu sojin Najeriya da ke cikin rundunar ta Sharan daji Reuters

Dakarun rundunar sojin Najeriya da ke cikin Operation Sharan Daji a Zamfara sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga 55 baya ga kubutar da mutane 760 wadanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su. 

Talla

Kamfanin dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito wata sanarwar rundunar sojin kasar mai dauke da sa hannun daraktan yada labaranta Manjo Janar Clement Abiade na cewa dakarunsu sun kuma yi nasarar kwace tarin makamai a hannun ‘yan bindigar.

Sanarwar ta ce dakarun sojin sun yiwa maboyar ‘yan tawayen kofar rago ne, lamarin da ya hana musu damar tserewa yayinda su kuma suka rika bude musu hutu.

A cewar rundunar yanzu haka ta kame wasu mutane 24 a cikin dajin wadanda aka yi ittifakin ko dai masu kai hare-hare kauyukan jihar ne ko kuma masu garkuwa da mutane, sai dai sanarwar ta ce suna ci gaba da bincike don hukunta su dai dai da laifunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.