Bakonmu a Yau

Malam Sani Rufa'i kan dambarwar siyasar Algeria bayan matakin Bouteflika na dage zaben kasar

Sauti 03:49
Dubban Al'ummar Algeria da ke ci gaba da bore kan matakin shugaban na dage zaben kasar daga watan gobe zuwa wani lokaci daban
Dubban Al'ummar Algeria da ke ci gaba da bore kan matakin shugaban na dage zaben kasar daga watan gobe zuwa wani lokaci daban AFP/Getty Images

A yau Juma'a dubun dubatar jama'a ne, suka sake gudanar da zanga zanga a birnin Algies na kasar Aljeriya, irinta ta farko tun bayan matakin da shugaban kasar Abduláziz Bouteflika ya dauka na daga ranar gudanar da zaben shugabancin kasar da aka shirya yi a ranar 28 ga watan Afrilun gobe. To domin jin yadda manazarta siyasar kasar ke kallon rikicin, da kuma irin tasirin da zai iya yi ga kasashe makwabtan kasar na larabawa Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Malam Sani Rufai, mai sharhi kan siyasar duniya, daga birnin Zinder na jahar Dmagaram a jamhuriyar Nijer ga kuma abinda yake cewa.