Burkina Faso

Ana bincikar sojin Burkina Faso kan zargin aikata laifukan yaki

Wasu dakarun rundunar sojin Burkina Faso.
Wasu dakarun rundunar sojin Burkina Faso. African Stand

Rundunar Sojin Burkina Faso ta kaddamar da bincike kan zargin da kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta yi kan wasu dakarunta, na yiwa wasu fararen hula kisan gilla ba da hakki ba.

Talla

Kungiyar ta Human Rights Watch, ta ce dakarun na Burkina Faso, sun aikata kisan gillar ne, yayin wani Samame da suka kai kan wasu yankunan arewacin kasar mai fama da hare-haren masu da’awar jihadi a watan Fabarairu, inda ta rundunar sojin kasar ta ce ta hallaka mayaka 146.

Human Rights Watch ta ce bayan gudanar da bincike, ta bankado cewa kusan mutane 60 daga cikin mayakan 146 an hallaka su ne a gaban Iyalansu ba tare da tabbatar da zargin da ake musu ba, na kasancewa ‘yan ta’adda.

Sai dai a martaninta, Gwamnatin Burkina Faso ta sha alwashin gudanar da sahihin bincike kan zargin.

A watan Disambar bara, gwamnatin Burkina Faso ta kafa dokar ta baci a wasu yankunan kasar da dama, bayan harin da wata kungiyar mayaka mai biyayya ga Al-Qaeda ta kai, a watan Janairun wannan shekara kuma aka tsawaita dokar ta bacin da Karin watanni 6, sakamakon barkewar rikicin Kabilanci a yankin arewacin kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.