Algeria

Masu zanga-zanga sun kafe kan aniyar tilastawa Bouteflika yin murabus

Masu zanga-zanga a Algeria.
Masu zanga-zanga a Algeria. Reuters/Zohra Bensemra

Dubban ‘yan Algeria sun sake fitar dango a babban birnin kasar Algiers, hadi da wasu biranen, inda suka sabunta zanga-zangar neman shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika yayi murabus.

Talla

Sabunta zanga-zangar, ya biyo bayan yunkurin shugaba Bouteflika na kwantar da hankulan ‘yan kasar, ta hanyar janye aniyar neman wa’adi na 5, amma da sharadin soke zaben shugabancin kasar da aka tsara yi a ranar 18 ga watan Afrilu, har zuwa wani lokaci cikin wannan shekara, inda zai sanar da sabon lokaci.

La’akari da cewa matakin ka ‘iya nufin Shugaba Bouteflika mai shekaru 82 zai iya kara tsawon shekara guda bisa shugabancin, yasa ‘yan kasar sabunta zanga-zangar tilasta masa yin murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI