Afrika

Yan Bindiga sun hallaka mutane a Mozambique

Filipe Nyusi, Shugaban kasar Mozambique
Filipe Nyusi, Shugaban kasar Mozambique Yasuyoshi CHIBA / AFP

Akalla mutane 13 ne aka bayyana cewa sun rasa rayukan su a arewacin kasar Mozambique bayan da wasu yan bindiga da ake zaton mayakan jihadi ne suka kai wasu kazaman hare-hare yankin Cabo Delgado.

Talla

An dai kai wadanan hare-hare ne kama daga ranar Alhamis,wanda aka kuma bayyana cewa maharan sun cinawa gidaje kusan 120 huta.

Kama daga shekara ta 2017,yankunan Cabo Delgado dake kan iyaka da Tanzania na daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro,wanda ake kuma zargin yan jihadi da kitsa wadanan hare-hare.

Shugabn kasar Filipe Nyusi ya bayar da umurnin don ganin an tura karin jami’an tsaro zuwa wadanan yankuna cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.