Najeriya-Atiku

Atiku ya nemi Kotu ta bayyana shi a wanda ya lashe zaben Najeriya

Dan takarar neman shugabancin Najeriya karkashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar
Dan takarar neman shugabancin Najeriya karkashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar AFP

Dan Takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar yau ya shigar da kara a gaban kotun, inda ya ke kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da aka yi ranar 23 ga watan nan.

Talla

Lauyoyin Abubakar tare da na Jam’iyyar PDP suka gabatar da takardun korafin inda su ke bukatar kotun ta soke sakamakon zaben da kuma bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara.

Dan takarar PDP ya sha alwashin daukar matakan shari’a domin kalubalantar sakamakon zaben da ya bayyana cewar shi ya samu nasara amma kuma hukumar zabe ta hada baki da gwamnatin APC wajen bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.

A baya-bayan nan ne dai Kotu a Najeriyar ta bai wa Hukumar zaben kasar mai zaman kan ta INEC umarnin barin dan takarar Atiku Abubakar isa ga takaddun zaben na ranar 23 ga wata don samun cikakkun hujjojin da zai kalubalanci sakamakon a gaban Kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.