Mali

Mahara sun hallaka sojojin Mali 21

Kididdiga ta nuna cewa a shekarar 2018, mayaka masu biyayya ga kungiyar Al-Qa'eda sun kaddamar da hare-hare sau 237 a sassan kasar Mali.
Kididdiga ta nuna cewa a shekarar 2018, mayaka masu biyayya ga kungiyar Al-Qa'eda sun kaddamar da hare-hare sau 237 a sassan kasar Mali. AFP

Sojojin Mali 21 ne suka rasa rayukansu a harin da ‘yan bindiga suka kai wa barikinsu na Dioura da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Talla

Harin shi ne mafi muni da mayakan da ake kyautata zaton cewa magoya bayan kungiyar Alqa’ida a yankin Macina ne suka kai wa wannan barikin soji a yanki Mopti da ke tsaiyar kasar.

Sanarwar daga ma’aikatar tsaron kasar ta Mali, ta ce ko baya ga kisan sojoji 21, a lokacin wannan hari da suka kai kafin wayewar safiya, maharan sun haddasa mummunar barna a wannan bariki kuma tuni aka yi jana’izar mamatan a marecen ranar Lahadi.

Binciken farko da rundunar sojin kasar ta fitar, na nuni da cewa maharan na karkashin jagorancin wani mai suna Ba Ag Moussa ne, wanda tsohon hafsan sojin kasar ne ya gudu sannan ya shiga ayyukan ta’addanci tun shekara ta 2012.

Ba Ag Moussa da wasu ake kira Bamoussa, babban na hannun damar jagoran kungiyar Alqa’ida a yankin Sahel ne mai Iyag Ag Ghaly, yayin da bayanai ke cewa maharan sun afka wa barikin na Dioura ne a kan babura da kuma motoci masu tarin yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI