Bakonmu a Yau

Bashir Ladan kan yunkurin jagoran 'yan adawa a Kamaru Maurice Kamto na tattaunawa da shugaba Paul Biya

Sauti 03:38

Jagoran ‘yan adawar kasar Kamaru Maurice Kamto da ke tsare a gidan yari bisa zargin cin amanar kasa, yana fatan shiga tattaunawa da shugaba Paul Biya don warware sabanin da ke tsakaninsu.Kamto, wanda ya zo na biyu a zaben shugabancin kasar da aka yi cikin watan Oktoban bara, ya ci gaba da nuna rashin amincewa da narasar Paul Biya, kafin daga bisani a cafke shi ranar 26 ga watan Janairun da ya gabata.Bashir Ladan, dan jarida kuma mai sharhi kan lamurran kasar ta Kamaru ya bayyana wa Zainab Ibrahim yadda yake kallon yunkurin na Maurice Kamto.