Najeriya-Bauchi

Kotu ta hana INEC sanar da sakamakon zaben Gwamnan Bauchi

A baya dai hukumar INEC ta ce za ta kammala tattarawa tare da sanar da sakamakon zaben ba tare da gudanar da sabo a ranar asabar 23 ga watan nan ba
A baya dai hukumar INEC ta ce za ta kammala tattarawa tare da sanar da sakamakon zaben ba tare da gudanar da sabo a ranar asabar 23 ga watan nan ba REUTERS/Adelaja Temilade

Wata Kotu a birnin Abuja da ke Najeriya, ta dakatar da hukumar zaben kasar INEC kan shirin ta na kammala tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke Bauchi, domin bayyana wanda ya samu nasara a zaben Gwamnan Jihar.

Talla

Alkali Inyang Ekwo ya bada umurnin dakatar da shirin bayyana sakamakon saboda bukatar haka da lauyan gwamnan Bauchi, Muhammad Abubakar ya gabatar a gaban sa.

Hukumar zaben Najeriya da farko ta bayyana cewar, sai an sake gudanar da zaben karamar hukumar Tafawa Balewa kafin sanin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, amma kuma daga bisani sai ta ce za ta koma ta sake tattara sakamakon zaben daga unguwanni zuwa karamar hukuma domin sanar da sakamakon.

Alkalin kotun ya kuma bada umurnin cigaba da shari’ar cikin gaggawa, inda ya bukaci masu karar da lauyoyin hukumar zabe da su gurfana a gaban sa gobe laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.