'Yan bindigan Zamfara na da makaman da Sojin Najeriya ba su da shi- Yari

Gwamnan Jihar Zamfara da ke Najeriya Abdulaziz Yari ya yi zargin cewar 'yan bindigar da su ke hallaka jama’a a Jihar sa baji ba gani, na da makaman da soji ba su da shi.

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari
Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari rfi hausa
Talla

Yayin ganawa da manema labarai, Gwamnan ya ce a wani rumbun aje makaman 'yan bindigar, an gano bindigogi kirar AK 47 sama da 500, yayin da wasu daga cikin Yan bindigar suka ki amincewa da tayin afuwar da gwamnati tayi musu.

Yari ya ce ya zuwa yanzu ba su iya karbar bindigogi sama da 90 daga wajen Yan bindigar ba, abinda ya sa gwamnatin sa ta yi watsi da shirin afuwar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI