Dr Sani Yahaya Janjuna kan barazanar tsaro a kasashen yammacin Afrika

Sauti 04:01
Wani banage na birnin Ougadougou a Burkina faso da ke fuskantar matsalar tsaro
Wani banage na birnin Ougadougou a Burkina faso da ke fuskantar matsalar tsaro Ahmed OUOBA / AFP

Yanzu haka dai barazanar da mayakan jihadin yankin Sahel ke haifarwa ta bazu zuwa kasashen kurmi da ke yammacin Afrika, inda ayukan kungiyoyin ya tsallaka Burkina Faso zuwa kasashen Togo, Ghana da kuma jamhuriyar Benin, inda a yan watannin da suka gabata aka samun hare haren taáddancin a yankunan da suka hada kan iyakokin kasashen.Domin jin yadda masharhantan tsaro ke kallon lamarin, Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Dr Sani Yahaya janjuna daga jamhuriyar Nijer, ga kuma tsokacin da ya yi mana.