Najeriya-Zabe

Sai 13 ga Aprilu za a sake zaben Gwamnan jihar Rivers- INEC

Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Farfesa Mahmud Yakubu Ventures Africa

Hukumar zaben Najeriya INEC ta tsayar da ranar 13 ga watan Afrilu, a matsayin ranar da za ta sake gudanar da zaben Gwamna da na ‘Yan Majalisun Jihar Rivers, bayan soke kuri’u da dama da aka kada yayin zaben da ya gabata a ranar 9 ga watan Maris.

Talla

Festus Okoye, babban jami’in lura da sashin wayar da kan masu kada kuri’a da yada labaran hukumar ta INEC, ya ce a ranar 2 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan, za a ci gaba da kidayar kuri’un da aka kada a zabukan na baya, aikin da aka dakatar saboda rikicin siyasa.

Hukumar zaben Najeriyar dai ta dakatar da tattara sakamakon zaben na Gwamnan jihar Rivers ne bayan tashe-tashen hankulan da aka fuskanta yayin zaben na ranar 9 ga wata.

Tun a wancan lokaci dai matakin na INEC ya haddasa zanga-zanga bisa zargin hukumar zaben na hada baki da jam'iyya mai mulki a Najeriyar APC don murde sakamakon zabe.

A ranar Asabar mai zuwa ne dai hukumar ta INEC za ta gudanar da zabe a yankunan da aka gaza kammala zaben Gwamna cikin jihohin kasar 6 ciki har da Kano da Bauchi da kuma Sokoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.