Burkina Faso

Rahoton HRW game da ayyukan mujahidai a Burkina Faso

Rahoton da kungiyar kare hakkin dan adam Human Rights Watch ta fitar a wannan juma’a, na nuni da cewa hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa sun yi sanadiyyar mutuwar dimbin mutane yayin da wasu dubbai suka bar muhallansu a Burkina Faso.

Rundunar sojin Burkina na binciken zargin da ake yi wa dakarunta na kashe jama'a
Rundunar sojin Burkina na binciken zargin da ake yi wa dakarunta na kashe jama'a African Stand
Talla

Rahoton kungiyar ta HRW ya ce hare-haren da masu da’awar jihadin ke kai wa kasar sun haddasa mummunar barna tare da haifar da rashin yarda a tsakanin al’ummomin kasar mai makotaka da Mali musamman daga tsakiyar shekara ta 2018 zuwa watan Fabarairun 2019.

Rahoton ya bayar da misali da yadda mayakan suke yin awun gaba da shugabannin al’umma tare da kashe akalla 42 daga cikinsu.

Yayin da suke wawashewa jama’a kadarori da kuma kwace masu dabbobinsu, sannan da kona makarantun boko, kwace motocin daukar marasa lafiya na wasu asibitoci a yankunan karkara da dai sauransu.

Kungiyar HRW ta ce wasu daga cikin hanyoyin da masu da’awar jihadin ke amfani da su domin razana jama’a sun hada hana bukukuwan aure ko suna, yayin da suke hana wa jama’a zuwa kasuwanni.

To sai dai wani bangare na rahoton ya zargin jami’an tsaron Burkina Faso da kashe akalla mutanen 115 a yankunan da ayyukan ta’addanci ya shafa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI