Nijar

Adadin mutanen da suka mutu a Diffa ya karu

Wasu daga cikin sojin Nijar da ke yaki da Boko Haram
Wasu daga cikin sojin Nijar da ke yaki da Boko Haram ISSOUF SANOGO / AFP

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da ‘yan Boko Haram suka kai a wasu kauyukan jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar sun kai 12 a cewar kungiyar kare hakkin bil’adama da ke yankin.

Talla

Jihar Diffa ta kasance daya daga cikin yankunan da yan Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare tare da kisan jama’a da dama.

Shugaban kasar Nijar Mamadou Issifou da jimawa ya dau alkawalin aikewa da dakarun kasar yankin ,mataki da ya taimaka wajen dawo da tsaro a wasu kauyuka,wanda hakan ya baiwa manoman yankin damar sake komawa ga ayukan noma.

Marah Mamadou jagoran kungiyoyin fararen hula ne a yankin na Diffa, wanda ya ziyarci daruruwan mutanen da suka samu mafaka a garin na Diffa ya na mai cewa.

Harin Boko Haram a Diffa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.