Alhaji Nouhou Abdou Magaji kan rikicin siyasar Algeria
Wallafawa ranar:
Sauti 03:38
A Algeria, bayan share makonni da dama ana gudanar da tarzomar neman shugaba Abdelaziz Bouteflika ya sauka daga karagar mulki, a jiya talata babban kwamandan askarawan kasar Janar Ahmed Gaid Salah ya bukaci a yi amfani da ayar doka mai lamba 102 ta kundin tsarin mulki, domin bayyana shugaban a matsayin wanda ba zai iya cigaba da mulki ba saboda rashin lafiya.A game da wannan mataki ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Nouhou Abdou Magaji Birnin Konni, masanin siyasar kasar ta Algeria.