Algeria

Ya zama wajibi shugaban Algeria yayi murabus - Sojoji

Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika tare da babban Hafsan sojin kasar Ahmed Gaid Salah a birnin Algiers. 11/3/2019.
Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika tare da babban Hafsan sojin kasar Ahmed Gaid Salah a birnin Algiers. 11/3/2019. AFP /Canal Algérie

Shugaban Hafsoshin sojin Algeria, Janar Ahmed Gaid Salah, ya bukaci aiwatar da doka ta 102 dake kundin tsarin mulkin kasar, wajen bayyana shugaba Abdelaziz Bouteflika a matsayin wanda rashin lafiya ta hana shi gudanar da ayyukansa, domin nada sabon shugaban kasa.

Talla

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar ta kafar talabijin, Janar Salah, yace daukar matakin ya zama wajibi domin kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar, ya kuma haifar da zanga zanga.

Shugaban sojin da Bouteflika ya nada a shekarar 2004, yace dokar ta 102 ta bayyana karara cewar ko shugaban kasa ya sauka da kansa, ko kuma a bayyana shi a matsayin wanda ba zai iya gudanar da aikin sa ba.

A makon da ya gabata Jam’iyyar Shugaban kasar Algeria Abdualziz Bouteflika, ta fito fili ta bayyana goyan bayan ta ga zanga zangar da ake yi na ganin ya sauka daga mulki da zarar wa’adinsa ya kare a watan gobe.

Matakin jam'yyar mai mulki, na daga cikin koma bayan da shugaban ke samu a yunkurin sa na cigaba da zama a karagar har zuwa karshen wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI