Rundunar Barkhane ta fadada aikinta na yakar ta'addanci a Mali
Wallafawa ranar:
Bayan shafe tsawon shekara guda da rabi ta na fafutukar samar da tsaro a garin Liptako dake yankin arewa maso gabashin Mali, rundunar musamman ta sojin Faransa “Barkhane”, dake yaki da ‘ya ta’adda a yankin Sahel, ta fadada aikinta zuwa garin Gourma da ke tsallaken kogin Nija, akan iyakar Mali da Burkina Faso.
Tun a shekarar 2017 Rundunar sojojin Faransar na Barkhane suke yakar gungun mayakan da suka yiwa kungiyar Al’qa’eda mubaya’a a garin Liptako dake kan iyakar Mali da Jamhuriyar Nijar, wanda kuma a yanzu sun cimma gagarumar nasara a cewar Janar Francois Lecointre, daya daga cikin manyan kwamandojin Dakarun na Barkhane, hakan yasa su fadada aikinsu zuwa Gourma.
A baya bayan nan dai mayakan masu da’awar jihadi sun kai munanan hare-hare kan sojojin Mali a Garin na Gourma dake kan iyakar Mali da Nijar, sakamakon karfi da mayakan kungiyar Ansarul Islam masu biyayya ga Al’qaeda suke dada samu a yankin na kudu maso gabashin kasar ta Mali.
A watan Nuwamban bara dakarun Faransa suka hallaka Al Mansour, shugaban kungiyar ta Ansarul Islam a wani farmakin da suka kai kan garin na Gourma, amma har yanzu mayakan suna ci gaba zama babbar barazana, saboda mafakar da suke samu a dazukan da ke kan iyaka da arewacin kasar Burkina Faso.
A shekarar 2012 Mali ta fuskanci barazanar tsaro mafi girma bayanda mayaka masu da’awar Jihadi suka kwace baki dayan yankin arewacin kasar, sai dai a 2013 sojojin Faransa na Barkhane suka yi nasarar dakile, amma har yanzu mafi akasarin yankin arewacin na ci gaba da kasancewa a karkashin mayakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu