Habasha

Matukan jirgin Habasha sun sha wuya kafin hatsarinsa

Wani rahoto ya bayyana cewa, jirgin Habasha da ya yi hatsari dauke da mutane 157 a watan jiya, ya sulmuyo da hancinsa daga sararin samaniya kafin daga bisani ya ci karo da doran kasa.

Wani bangare na baraguzan jirgin da ya yi hatsari a Habasha
Wani bangare na baraguzan jirgin da ya yi hatsari a Habasha REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Rahoton na wucen-gadi ya bayyana cewa, matukan jirgin sun yi iya bakin kokarinsu don kauce wa aukuwar hatsarin, kuma sun mutunta sharuddan da makeran jirgin na Boeing suka shimfida.

Ministar Sufurin Habasha, Dagmawit Moges ta ce, matukan jirgin sun gaza shawo kan wannan jirgi duk kuwa da kokarinsu na ganin sun samu nasara.

Jirgin mai lamba ET302 ya yi hatsari ne jim kadan da tashinsa daga birnin Addis Ababa, in da ya kashe daukacin mutanen da ke cikinsa.

A karo na biyu kenan da irin wannan jirgin samfurin Boeing 737 Max ke hatsari a cikin watanni biyar.

A cikin watan Oktoban da ya gabata, irin samfurin jirgin ya yi hatsari a Indonesia tare da kashe mutane 189.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI