Ko kaho da wanzamai ke yi na da alfanu ko akasin haka?
Wallafawa ranar:
Sauti 19:57
Shiri ne da ke amsa tambayoyin masu sauraro kamar yadda suka aiko mana, kuma yake zuwa muku duk mako,ta sashen Hausa na Radio France Internationale, naku, Michael Kuduson ke cewa a yi sauraro lafiya.Sani Mailengelenge, Yelwa Yauri a jihar Kebbin Najeriya, ya ce a tambaya mana likita ko kaho da wanzamai ke yi na da alfanu ko akasin haka? Ko akwai abin da yayi kama da kaho a likitance?